An bude gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya

Bikin bude gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya
Image caption Daruruwan makada da masu raye-raye ne suka hallarci bikin

An bude gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya a Afrika ta Kudu ta hanyar gudanar da wani kasaitaccen biki a filin wasan Soccer City dake birnin Johannesburg.

Daruruwan makada da mawaka da masu rawa suka yi wasa mai ban sha'awa.

Wannan shi ne karo na farko da ake gudanar da wannan gasa a nahiyar Afrika, kuma kasashe talatin da biyu ne za su fafata a wannan gasa a cikin wata guda mai zuwa.

Sai dai tsohon shugaban Afrika ta Kudu Nelson Mandela bai sami damar halartar wannan gasa ba saboda rasuwar wata tattaba kunnensa, sakamakon wani hadarin mota a jiya.