Argentina ta yi nasara kan Nijeriya

Wasan da aka yi tsakanin Nijeriya da Argentina
Image caption Wasan da aka yi tsakanin Nijeriya da Argentina

Kasar Argentina ta yi nasara kan Nijeriya a karawar da suka yi a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya a Afrika ta Kudu.

Argentina din dai ta yi nasara ne a kan Nijeriya da ci daya da nema.

Hakan na nufin cewa Argentina ita ce ta biyu a rukunin B, bayan da Koriya ta Kudu tai nasara kan kasar Girka da ci biyu ba ko daya.

An taka leda sosai a wannan wasa wanda Nijeriya ta sami damammaki da dama amma ba tai amfani da su ba.