Hare-Haren gungun 'yan kwaya a Mexico

Hare-Haren 'yan kwaya a kasar Mexico
Image caption Kusan mutane arba'in ne suka hallaka bayan wani hari da aka kai dake da akala da na 'yan kwaya a Mexico

Kusan mutane arba'in ne suka halaka sakamakon hare harenda suke da alaka da masu safarar miyagun kwayoyi a kasar Mexico.

An tsinci gawarwaki ashirin a arewa maso gabashin birnin Ciudad Madero, wadanda dukkaninsu harbe su aka yi, sannan wasu daga cikinsu akwai alamun cewa sai da aka azabtar da su.

Da farko dai a birnin Chihuahua dake arewacin Mexico, yan bindiga sun halaka mutane 19, a wata cibiyar kula da yan kwaya.

Daga kasar Afirka ta kudu inda yake halartar bikin bude gasar cin kofin kwallon kafar duniya, shugaba Felipe Calderon ya aike da wata sanarwa inda yayi Allawadai da abinda ya auku.

Shugaban ya kuma ce wannan na kara nuni da cewar dole ne a tashi tsaye wajen yakar masu ta'ammali da miyagun kwayoyin da karfin tsiya