Rikicin Kygyzstan ya watsu zuwa kudanci

Wani yaro dan kabilar Uzbek da aka raunata
Image caption Wani yaro dan kabilar Uzbek, wanda rahotanni suka ce jam'ian tsaron Kyrgyzstan sun harba a gadon asibiti a kauyen Naramon da ke kusa da filin jirgin saman Osh

Kididdiga ta baya-bayan nan ta bayyana cewa yawan mutanen da suka mutu a tashe-tashen hankula na kabilanci da suka barke a gari na biyu mafi girma a kasar Kyrgyzstan, wato Osh, ya karu.

Sababbin alkaluman da ma'aikatar lafiya ta kasar ta fitar yau Lahadi sun nuna cewa kusan mutane tamanin ne suka rasa rayukansu, yayinda wasu mutanen fiye da dubu daya suka yi rauni a rikicin kabilancin.

Hukmomin sun kuma ce rikicin ya watsu zuwa garin Jalalabad da ke kudancin kasar.

Jiya Asabar ne dai gwamnatin rikon kwarya ta kasar ta umurci sojoji su fita don kwantar da rikicin; ta kuma ba jami'an tsaro umurnin su harbe duk wanda suka gani da makami.

Kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Amnesty International ta ce wadanda suka shaida al'amarin sun bayar da labarin cewa 'yan kabilar Kyrgyz dauke da makamai na kai hari a kan 'yan kabilar Uzbek, suna kuma kona musu gidaje.

Gwamnatin Kyrgyzstan din dai ta nemi taimakon Rasha don kawo karshen rikicin; sai dai Rashan ta ce za ta aike da kayan agaji ne kawai, amma ba za ta aike da dakaru ba tukuna.

Wannan dai shi ne tashin hankali mafi muni a kasar tun bayan kifar da gwamnatin Kurmanbek Bakiyev a watan Afrilun da ya gabata.

Karin bayani