Rikicin Kyrgyzstan ya kazance

Rikicin Kyrgyzstan
Image caption Rikicin Kyrgyzstan

Rikicin da ake yi tsakanin 'yan kabilar Kyrgyz da na Uzbek a kudancin Kyrgyzstan ya kazance inda akai mummunan dauki ba dadi a kewayen Osh, birni na biyu mafi girma a kasar.

An kona gine-gine a yankunan birnin da 'yan Uzbek marasa rinjaye ke zaune, har ma da wasu kauyuka da 'yan kabilar Uzbek din ke zaune. Wadanda suka shaida da idanunsu sun ce sun ga gawawwaki a kan tituna.

An tabbatar cewa akalla mutane 80 aka kashe a tashin hankalin.

Wakiliyar BBC ta ce akwai daruruwan jama'a, mata da kananan yara a yankin kan iyaka tsakanin Uzbekistan da Kyrgyzstan, kuma suna bukatar taimako ainun.

Wannan rikici dai ya sa ana nuna fargaba ta yiwuwar bazuwar tashin hankali a duk fadin kasar ta Kyrgyzstan, inda Rasha da Amirka ke da sansanonin soja.