Ma'aikatan Stirling sun shiga mawuyacin hali

Nigeria
Image caption Nigeria

A jihar Bornon Nijeriya, kimanin ma'aikatan kamfanin gine-gine na kasar Italiya wato Stirling Civil Engineering kusan dari hudu ne suka shiga mawuyacin hali bayan rufewar da kamfanin ya yi ya kama gaban sa, ba tare biya mu su hakkokin su ba.

Ma'aikatan daga sassa daban-daban na jihar Bornon ne suka hallara a cikin garin Maiduguri domin gudanar da gangamin kira ga kungiyoyi kare hakkin jama'a da hukumomi na su agaza wajen bi musu wadannan hakkoki nasu da suka shafe kusan shekaru hudu suna bi.

Ita dai Kungiyar Civil Liberties Oraganization dake Jihar Borno tace zata fara gudanar da bincike a wani kamfanin gine-ginen da aka bayyana ya gaji ayyukan kamfanin na kasar Italiya a jihar domin daukar matakan da suka dace.