Majalisun dokokin Arewa sun nemi a yi zabe ingantacce

Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan
Image caption Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan

An gudanar da taron shugabannin majalisun dokokin jihohin arewacin Najeriya karo na 20 a Dutse babban birnin jihar Jigawa dake Najeriya.

Taron yayi kira ga shugaban Nijeriya Dr Goodluck Jonathan da ya tabbatar an gudanar da zabe na gari a shekara ta 2011.

Bugu da kari taron yayi alkawarin hanzarta duba batutuwan da suka shafi gyaran tsarin mulki.

Hakazalika, sanarwar bayan taron ta yi tsokaci kan halin da aka shiga a jihar Zamfara game da rasuwar mutane sama da dari da sittin, sakamakon shakar gubar sinadarin dalma, da kuma rikicin jihar Filato da ya ki ci ya ki cinyewa.