Rasha ta tura karin sojoji Kyrgyzstan

Kyrgyzstan
Image caption Kyrgyzstan

Jami'ai a Rasha sun ce gwamnatin kasar ta tura karin sojoji zuwa Kyrgyzstan yayinda rikicin kabilanci ke kara kazancewa a Kudancin kasar.

Sun ce sojojin za su kare sansanin sojan Rashar ne dake Arewacin kasar ta Kyrgyzstan da kuma kare lafiyar jami'an tsaron Rashar dake can tare da iyalansu.

Da ma dai gwamnatin Kyrgyzstan din ta nemi Rasha da ta tura sojojinta zuwa kasar, amma Rashar ta ce ba za ta dauki mataki ita kadai ba.

Kungiyoyin kabilar Kyrgyz dai sun yi ta kai hare-hare akan 'yan kabilar Uzbek marasa rinjaye, musamman a Osh, birnin na biyu mafi girma a kasar.

An kona gine-gine a birnin, kuma wadanda suka shaida sun ce sun ga gawaki a kan tituna.

Kusan mutane 100 ne dai aka tabbatar an kashe a tashin hankalin.