Ranar bada gudummawar jini ta duniya

Wani matashi na bada gudunmayar jini a Kabul na Afghanistan
Image caption Wani matashi na bada gudunmayar jini a Kabul na Afghanistan

Yau ce ranar da majalisar dinkin duniya ta kebe, domin fadakar da jama'a a kan muhimmancin bada gudunmawar jini, domin ceto rayukan jama'ar da ke shiga mawuyacin hali.

Taken bikin na bana dai shine ''Sabon Jini ga Duniya'' , wanda wani kira ne ga matasa da su kara hobbasa wajen bada gudunmawar jinin.

Albarkacin wannan ranar, Cibiyar Bayar da Jini ta Nigeria, shiyyar arewa maso gabashin kasar, wadda ke Asibitin Koyarwa na Jami'ar Maiduguri, ta gudanar da wani taron lacca da kuma gangami a Maidugurin, domin fadakar da jama'a akan alfanun bada jini.