Mutane biyar sun mutu a Nairobin Kenya

Shugaba Mwai Kibaki na Kenya
Image caption Shugabannin addinin Kirista da 'yan siyasa masu adawa da sabon kundin tsarin mulkin Kenya ne suka shirya gangamin

Akalla mutane biyar ne suka rasa rayukansu, yayinda wadansu da dama kuma suka jikkata, sakamakon turmutsutsun da ya biyo bayan fashewar wasu bama-bamai a wajen wani gangami a babban birnin kasar Kenya, Nairobi.

Har yanzu dai fashewar wadannan bama-bamai biyu na da daurewar kai.

'Yan sanda sun ce bama-baman kanana ne, kuma suna zaton a gida aka hada su.

Fashewar bama-baman dai ta auku ne lokacin da dubun dubatar mutane suka taru a wani dandali a tsakiyar birnin Nairobi don halartar wani taron addu'a wanda shugabannin addini da wadansu 'yan siyasa masu adawa da sabon kundin tsarin mulkin kasar suka shirya.

Mutanen dai na adawa ne da sassan kundin tsarin mulkin da suka shafi zubar da ciki da kuma kafa kotunan shariar Musulunci.

A watan Agusta ne dai ake sa ran al'ummar Kenya za su kada kuri'ar raba gardama a kan sabon kundin tsarin mulkin.

Ga alamu dai firgici da turereniyar da fashewar ta haifar ne suka haddasa yawancin raunukan da mutane suka ji.

Daurewar kan da al'amarin ya haifar ta karu lokacin da aka gano gawar wani mutum da aka harba da bindiga a cikin wata mota bayan kowa ya watse.

Sai dai har yanzu babu tabbas a kan ko fashewar bama-baman na da alaka da takaddamar da ake yi a kan sabon kundin tsarin mulkin.