An yi kiran a bullo da hukuncin kisa ga masu cin hanci da rashawa a Najeriya

Shugaba Goodluck Jonathan
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya

Shugaban taron shugabannin majalisun dokokin jihohin arewacin Najeriya, Alhaji Gwani Madu, yayi kiran da a bullo da dokoki masu tsauri, ko da ma hukuncin kisa ne, domin magance matsalar cin hanci da rashawa a kasar.

Alhaji Gwani Madu wanda kuma shi ne kakakin majalisar dokokin jihar Borno, ya koka kan yadda wasu manyan 'yan kwangila ke kin yin ayyukan raya kasa da aka basu, bayan sun karbe kudaden kwangilar.

Ya ce, bullo da hukunci mai tsauri zai taimaka wajen rage annobar ta cin hanci da rashawa da ta addabi al'umar Najeriya.

Alhaji Gwani madu ya bayar da misali da kasar China inda ake yanke hukuncin kisa a kan duk wanda aka samu da laifin cin hanci da rashawa.