Kungiyar Red Cross ta soki Isra'ila

Harin dakarun Isra'ila kan jiragen ruwa dauke da kayan agaji
Image caption Sukar kungiyar Red Cross a kan Isra'ila alama ce ta karuwar damuwa dangane da killace Gaza da Isra'ila ta yi

Kungiyar bayar da agaji ta Red Cross ta ce killace Zirin Gaza da Isra'ila ta yi ya sabawa dokokin kasa-da-kasa.

A wata sanarwa mai cike da suka da ba a saba ganin irinta ba, kungiyar ta Red Cross, wadda ba kasafai ta kan nuna goyon baya ga wani bangare ba, ta ce Isra'ila na ganawa daukacin al'ummar Gaza ukuba saboda wani laifi da ba su suka aikata ba.

Wannan, a cewar kungiyar, a zahiri ya sabawa dokokin kare hakkin bil-Adama na kasa-da-kasa.

Kungiyar ta Red Cross ta bayyana irin mummunan yanayin da al'ummar Gaza ke ciki, inda suke fama da karancin magunguna da sauran kayan aiki a asibitoci, da karancin wutar lantarki, da kuma rashin tsaftataccen ruwan sha.

Kungiyar ta kuma zargi kungiyar Hamas da laifin saba dokar kasa-da-kasa ta hanyar kin barin jami'anta su ziyarci wani sojan Isra'ila, Gilad Shalit, wanda Hamas din ke tsare da shi kusan tsawon shekaru biyar.

Ta kuma dora alhakin wadansu daga cikin wahalahalun da ake fama da su a Gaza a kan bambance-bambancen da ke tsakanin Hamas da hukumar mulki ta Falasdinawa.

Sai dai kashin bayan sanarwar kungiyar ta Red Cross, wadda ba kasafai ta kan soki gwamnatocin kasashe ba, shi ne: wajibi ne Isra'ila ta kawo karshen killace Zirin Gaza.

Wannan sanarwar kuma wata alama ce da ke nuna yadda al'ummar duniya ke kara damuwa da halin da al'ummar Gaza ke ciki.

Ko a makon da ya gabata, Shugaba Obama na Amurka ma ya bayyana killacewar ta Isra'ila da cewa ba mai dorewa ba ce.