Malamai sun nemi a sako Dr Ahmed Gummi.

Masallacin Abuja, Nijeriya.
Image caption Daya daga cikin masallatai mafiya girma a Nijeriya.

A Nijeriya wasu malaman addinin Musulunci sun yi kira ga hukumomin kasar da su tsoma baki domin ganin an sako mai wa'azin musuluncin nan Dr Ahmed Mahmud Gummi, wanda hukumomin Saudiyya ke tsare da shi.

Malaman addinin Musulunci, karkashin inuwar majalisar koli ta shari'a, da reshen kungiyar Izalatul Bidi'a da kuma wasu mambobin majalisar Malamai ta kasa sun gabatar da wannan roko ne a Kaduna, inda suka kira wani taron manema labaru.

A halin yanzu dai Sheikh Gumi ya shafe watanni yana tsare a Saudiyyar, kan zargin da hukumomin kasar ke cewa na da nasaba da batun tsaro, amma ba tare da sun yi cikakken bayani ba.