'Rikicin Kyrgyzstan shirya shi aka yi'

Gidaje na cin wuta a Kyrgyzstan
Image caption Ana ci gaba da kona dukiyoyi a kudancin Kyrgyzstan

Kungiyoyin bayar da agaji da na kare hakkin bil-Adama sun yi kira da a kawo karshen tashe-tashen hankula a Kyrgyzstan.

Kwamishiniyar kare hakkin bil-Adama ta Majalisar Dinkin Duniya, Navi Pillay, ta ce tana da labarin cewa an yi kisan kan mai-uwa-da-wabi a kan mutane da dama ciki har da kananan yara; an kuma yiwa mata fyade a kudancin kasar ta Kyrgyzystan.

A cewarta, alamu sun nuna cewa da manufa aka shirya tashe-tashen hankulan don kashe wasu bayin Allah.

Ta yi kira ga hukumomin Kyrgyzystan su dauki kwararan matakan kawo karshen al'amarin.

Sai dai ta ce umurnin da gwamnatin kasar ta bayar na yin harbi don kisa ba shi zai kawo maslaha ba.

A cewarta, bai kamata a yi watsi da ka'idojin kare hakkin bil-Adama ba a ko a wanne irin yanayi.

A halin da ake ciki kuma, kungiyar bayar da agaji ta Red Cross ta ce ma'aikatan ta sun kasa shiga garin Jalalabad ranar Litinin saboda tsananin harbe-harbe.

Image caption Dubban mutane ne ke jiran samun damar ketarawa Uzbekistan

Kungiyar ta ce akalla mutane dari da ashirin da hudu ne suka mutu a kwanaki ukun da suka wuce a saninta, sai dai ta ce mai yiwuwa yawan wadanda suka mutun ya fi haka.

Wani babban jami'in kungiyar ta Red Cross ya ce yawan wadanda suka mutun kuma ka iya karuwa.

An kiyasta cewa mutane dubu tamanin ne suka ketare iyakar kasar da Uzbekistan, yayinda wadansu mutanen dubu goma sha biyar ke jiran damar tsallakawa.