Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya na shirin kai agajin gaggawa a kasar Uzbekistan

Gidaje na cin wuta a Kyrgyzstan
Image caption Ana ci gaba da kona dukiyoyi a kudancin Kyrgyzstan

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya, na shirye-shiryen kai kayayyakin agaji na gaggawa ta jiragen sama, a kasar Uzbekistan, domin taimakawa 'yan gudun hijirar da ke ta tudada zuwa can daga Kyrgyzstan.

Hukumar 'yan gudun hijirar ta ce, fiye da mutane dubu dari biyu da hamsin ne suka gujewa rikicin kabilancin da ake yi a kudancin Kyrgyzstan.

Kimanin dubu saba'in da biyar daga cikinsu sun samu sun tsallaka iyaka zuwa Uzbekistan.

Tun farko dai kungiyoyin bayar da agaji da na kare hakkin bil-Adama sun yi kira da a kawo karshen tashe-tashen hankula a Kyrgyzstan.

Kwamishiniyar kare hakkin bil-Adama ta Majalisar Dinkin Duniya, Navi Pillay, ta ce tana da labarin cewa an yi kisan kan mai-uwa-da-wabi a kan mutane da dama ciki har da kananan yara; an kuma yiwa mata fyade a kudancin kasar ta Kyrgyzystan.

A cewarta, alamu sun nuna cewa da manufa aka shirya tashe-tashen hankulan don kashe wasu bayin Allah.

Ta yi kira ga hukumomin Kyrgyzystan su dauki kwararan matakan kawo karshen al'amarin.

Sai dai ta ce umurnin da gwamnatin kasar ta bayar na yin harbi don kisa ba shi zai kawo maslaha ba.

A cewarta, bai kamata a yi watsi da ka'idojin kare hakkin bil-Adama ba a ko a wanne irin yanayi.

A halin da ake ciki kuma, kungiyar bayar da agaji ta Red Cross ta ce ma'aikatan ta sun kasa shiga garin Jalalabad ranar Litinin saboda tsananin harbe-harbe.

Image caption Dubban mutane ne ke jiran samun damar ketarawa Uzbekistan

Kungiyar ta ce akalla mutane dari da ashirin da hudu ne suka mutu a kwanaki ukun da suka wuce a saninta, sai dai ta ce mai yiwuwa yawan wadanda suka mutun ya fi haka.

Wani babban jami'in kungiyar ta Red Cross ya ce yawan wadanda suka mutun kuma ka iya karuwa.

An kiyasta cewa mutane dubu tamanin ne suka ketare iyakar kasar da Uzbekistan, yayinda wadansu mutanen dubu goma sha biyar ke jiran damar tsallakawa.