Masu fafutuka sun nemi gwamnan Abia ya sauka

Nijeriya
Image caption Nijeriya

A Nijeriya, gungun wasu kungiyoyi guda bakwai na masu fafutukar kare hakkin bil'Adama da rajin kare tsarin dimukuradiyya, ya nemi gwamnan jihar Abiya, Cif Theodore Orji ya sauka daga mukaminsa.

Matsalar yawan aukuwar miyagun laifuffuka da kuma zargin rashin katabus wajen samar da ababen more rayuwa a jihar na daga cikin matsalolin kungoyoyin sukai kuka akai. .

Sai dai bangaren gwamnan yana ganin wannan kira bai dace ba, don haka ya yi watsi da shi.