Ranar kare hakkin kananan yara a nahiyar Afirka

Yara a nahiyar Afirka
Image caption Yara a nahiyar Afirka

Kasashen Afirka na tunawa da kashe-kashen Soweto na 1976, lokacin da jami'an tsaro suka hallaka wasu dalibai masu zanga-zanga a Afirka ta Kudu.

'Yan makarantar na nema ne a kyautata yanayin karatun su, lokacin da jami'an tsaron suka bude masu wuta, tare da hallaka wasunsu.

Kungiyar Tarayyar Afirka ta kebe wannan ranar ce, domin jawo hankalin jama'a akan hakkokin kananan yara a dukan fadin nahiyar.

Gwamnatin Niger tace an sami cigaba wajen kyautata rayuwar kananan yara a kasar.

Sai dai wasu kungiyoyi masu fafutukar kare 'yancin yaran na ganin cewa har yanzu akwai matsalolin da ba a shawo kansu ba - alal misali, a fannonin ilimi da kiwon lafiya, da kuma wajen fataucin kananan yaran.