Shugabannin addinai a Afirka na neman zaman lafiya

Taron kolin Tarayyar Afirka
Image caption Taron kolin Tarayyar Afirka

Shugabannin addinai daga nahiyar Afirka na ganawa a karkashin kungiyar Tarayyar Afirka, domin duba hanyoyin da ya kamata a bi, wajen shawo kan tashe tashen hankulan dake aukuwa, masu nasaba da addini.

Wakilan addinai daga sassa dabam-dabam na nahiyar Afirka ne ke halartar taron, wanda ake yi a babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja.

Rikice rikicen addini na janyo hasarar dimbin rayuka da hasarar dukiya a nahiyar Afirka, musamman a Najeriya.

Masana na ganin cewa, rashin fahimtar juna tsakanin addinai, na daga cikin manyan dalilan da ke janyo rikici tsakanin mabiya addinai dabam-dabam.