Gwamnatin Nijeriya zata rarraba biliyan 365

Kudin Nijeriya
Image caption Kudin Nijeriya

Gwamnatin Nigeria ta kasafta yadda zata rarraba kimanin Naira biliyan 365 a tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi da kananan hukumoni, domin su aiwatar da ayyukansu.

Sannan kuma ta bayyana bude wani asusu na musamman domin ajiye sauran rarar kudaden da suka rage.

Wannan dai yana faruwa ne a daidai lokacin da gwamnatin kasar ke kokarin sake lale akan farashin da ta kayyade akan danyan mai, wanda kuma da shi ne take samun mafi yawan wadannan kudaden.