Majalisar dinkin duniya ta dakatar da agaji zuwa Zambiya

Magunguna
Image caption Asusun bada tallafin na bada agajin magungunan domin yaki da cutar HIV da AIDS da tarin fuka.

Asusun majalisar dinkin duniya na yakar cutar kanjamau da tarin fika da zazzabin cizon sauro, ya dakatar da agajin dala miliyan 300 da ya saba bayarwa domin yakar cututtukan a zambiya.

Asusun ya ce ya damu da rahotannin cin hanci da rashawa da ke da alaka da tallafin da ake baiwa ma'aikatar kiwon lafiya da kasar ta Zambiya.

Sanarwar asusun ta kara da cewa zai ci gaba da bada tallafi domin yakar cututtukan da ke barazana ga lafiyar jama'a, amma zai bada kudin ne kai tsaye ga masu samar da magunguna ba mahukuntan kasar ba.

Asusun ya ce gwamnatin ta kasa bada tabbacin cewa za ta dauki matakan kawar da cin hancin, wanda ke kawo cikas ga ayyukan agajin.

Cin hanci

Asusun kassahen duniyan ya ce hukumomi a Zambia sun kasa samar da tabbaci na cewar suna daukar dukkanin matakan da suka dace domin ganin cewar ba'a karkartar da akalar kudaden da ake baiwa kasar ta hanyar da bata dace ba.

Dakatarwar bayarda miliyoyin dalolin domin tallafawa shirin kula da lafiyar kasar zai kasance wani babban komabaya ga kasar da take dogaro da tallafi, wacce kuma cututuuka irinsu HIV da kuma AIDS su kai wa kanta.

Wannan dai bashi bane karo na farko da asusun ya dakatar da tallafin nasa ga Afirka ba.

Asusun ya dau irin wannan mataki akan kasar Uganda shekaru biyar da suka gabata saboda rashin gamsuwarsa game da yadda hukumomin kasar suke tafiyarda kudaden da asusun ya bayar.

Asusun tallafi

An dai kafa wannan asusu na Global Fund a shekarra 2002 karkashin shugabancin tsohon babban sakataren majalisar dinkin duniya Kofi Anan.

Asusun ya rarraba kayayyakin tallafi na fiye da dala biliyan goma sha tara da nufin yakar cututtuka irinsu HIV, malaria da kuma tarin fuka.

Asudun dai na samun kudadensa ne daga gwamanti da kuma wasu hanyoyi wanda bana gwamanti ba. Kuma asusun na maida hankalinsa ne kan kassahen afirka masu fama da talauci mafiyawancin su wadanda ke Afirka ta kudu da hamadar sahara inda cin hanci da rashawa ya zama ruwan dare.

Amma Dangane da kasar Zambia kuwa asusun yasha yiwa gwamantin kasar gargadi na cewar ta gyara al'amauranta.

Sai dai zambian tayi watsi da wannan gargadi. Ko a shekarar data gabata kungiyar tarayyar turai ta dakatar da bada wasu kudade data ware domin gina tituna a kasar saboda cin hanci kuma duka dai a shekarar data gabatan kassahen Newzeland da Sweden sun dakatar da dala miliyan talatin da aka ware ga ma'aikatar lafiyar zambian saboda ganin yadda kudade suke layar zana a tsakankanin jami'an kasar.