Obama ya gana da shugabannin BP

Obama na ganawa da jami'an kamfanin BP
Image caption Obama na ganawa da jami'an kamfanin BP

Shugaba Obama ya yi wata ganawar ido da ido, da shugabannin kamfanin mai na BP, watanni biyu bayan da wata rijiyar man kamfanin ta yi bindiga, ta kuma haddasa barna mafi girma ga muhalli a Amurka.

Miliyoyin galan galan na mai ne ya kwarara cikin tekun Mexico, tun bayan fashewar da aka samu a rijiyar man cikin watan Afrilu, inda mutane goma sha daya suka mutu.

Yau da yamma ne shugaban kampanin na BP, Tony Hayward, wanda yayi ta fuskantar suka kan tsiyayar man, ya shiga fadar White House, domin yin bayani kan yadda kamfanin zai toshe bututun man dake zubar da mai, da biyan diyya ga wadanda abin ya shafa, da kuma dawo da martabar kampanin a Amurka. Akwai dai rahotannin dake cewa BP din ya amince da ya ware dala biliyan 20, ko fam biliyan 14, domin biyan diyya kan barnar da aka yi wa muhalli, da hanyar abincin mutane masu yawa a gabar teku.