Mazauna garin Madorawa sun bijirewa ginin jami'a

Zanga zangar bijirewa ginin jami'a
Image caption Jama'ar garin dai na korafi ne a bisa makomar gonaki da kuma gidajen su

Mazauna kauyen Madorawa da ke wajen birnin Sakkwato a Arewacin Najeriya sun yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da shirin gwamnatin jahar na sauya mazaunin kauyen domin kafa jami'a.

Gwamantin dai na son yin hakan ne domin kafa jami'a mallakin jihar ta Sokkwato.

Masu zanga zangar wadanda yawancinsu manoma ne sunce kafa jami'ar a wurin zai raba su da gonakkinsu masu albarkar kasar noma.

Kazalika da kuma tarwatsa al'ummar da ta dauki fiye da karni guda tana zaune a wuri guda.

Gwamnatin jahar dai tace ta yanke shawarar kafa jami'ar ne da amincewar wasu shugabannin al'ummomin.

Dimbin mazauna kauyen sun fito dauke da ganyaye domin nuna rashin amincewar su da shirin gwamnatin jahar na tayarda kauyukkan domin kafa jam'ia.

Image caption An dade ana zargin mahukuntan Najeriya da tayar da jama'a daga matsugunen su

Malam Umaru Madorawa wani magidanci na daga cikin masu zanga zangar kuma yayi ma wakilin BBC Haruna Tangaza, bayanin dalilinsu na daukar wannan matakin.

Yace muna yin zanga zangar ne domin nuna adawar mu da gina makarantar anan, saboda ba za ayi mana adalci ba.

Ya kuma musanta cewa gina jami'air zai taimaka musu, yana mai cewa an gina filin saukar jiragen sama a baya amma bai amfana musu komai ba.

Ko baya ga wadannan batutuwan dai rashin son rabuwa da ababen tarihi na daga cikin abubuwan da suka sa mutanen ke adawa da kafa wannan jami'ar kamar yadda wannan mai zanga-zangar ya bayyana.

Yace su ba kudi suke bukata ba, illa dai kawai abar su su ci gaba da zama a garin su.

"babu wanda ya isa ya hana"

Farfesa Gajam Ardo Shi ne shugaban hukumar kula da ilmi mai zurfi ta jahar, ya kuma yi watsi da kalaman mutanen.

"Wannan ba gaskiya ba ne, 'yan adawa ne kawai, ba sa so mu gina jami'a a jihar nan.

Sannan yace babu wanda ya isa ya hana a gina jami'ar sai Allah madaukakin sarki.

Abin jra dai again shine wanda zai dau girma ganin cewar bangarorin biyu sun ja daga.