Mace ta jagoranci sallar Juma'a a Burtaniya

Limamiya Mace
Image caption Raheel Raza tana limanci a wani masallacin Juma'a a garin Oxford na Burtaniya

A makon da ya gabata ne wata mata 'yar kasar Canada tayi tattaki zuwa garin Oxford na Burtaniya domin jagorantar sallar Juma'a.

Sai dai malaman addinin musulunci daga sassa da daban daban na duniya sun yi Allah wadai da aikin nata, suna masu cewa ya sabawa koyarwar Annabi Muhammad Tsira da aminci su tabbata a gareshi.

Raheel Raza ta fara jagorantar sallar da ta hada jinsin maza da mata a Canada shekaru biyar da suka gabata.

Raheela ta bayyana aniyar ta kalubalantar mamayar da maza suka yi a harkokin addini a masallatai.

Matsayin addinin musulunci

Ustaz Zakariyya, malamin addinin musulunci ne a Abuja, kuma yace addinin musulunci anayin sa ne ta hanyar koyi da Annabi Sallahu Alaihi Wasallam.

Ya shaidawa wakilin BBC Jimeh Saleh cewa, duk da dai akwai masu mazahabobi da suka ce mace za ta iya yin limanci a cikin gida, amma addinin musulunci ya hana.

"Wannan fitina ce da ake son bullowa da ita a cikin al'ummar musulmi".

Ya kara da cewa babu wani hukunci da za a iya fitowa da shi idan har babu shi alokacin Annabi.

Yace sallar mace a kuryar dakin ta tafi lada, fiye da a falonta, ballantana ma awaje.

"Musulunci ya hana haduwa tsakanin maza da mata, kuma wannan hukunci yana nan, babu wanda ya isa ya gogeshi, indai maganar musuluncin gaske ake yi," in ji Ustaz Zakariyya.

Hira da BBC

Ta zamo mace ta farko musulma data jagoranci sallah a Burtaniya, ta kuma gayawa wakiliyar BBC Lucy Ash cewa tana alfahari da hakan.

Tace nayi limanicin sallar farko a Canada, kimanin shekaru biyar da suka gabata.

Kuma wannan ya faru ne bisa ga kiran da wata kungiyar Musulmai dake can, wadda ake kira Muslim Canadian Congress ta yi min.

Kungiyar na duba irin yanda ake barin mata a baya, da kuma rashin baiwa mata 'yancinsu da Al Qurani ya tanada.

Don haka ne suke so su aikewa maza da mata da wani sako, don haka ne suka gayyace ni dana jagoranci Sallah.

Wannan kuma ya faru ne bayan da Amina Wadud tayi limancin Sallar farko a New York. Don haka ne na amince, kuma tun daga wannan lokacin nake jagorantar sallah a Canada da New York, wannan ne dai karo na uku.

Image caption Raheela tana yiwa mabiyanta kuduba

Ko da aka tambayeta cewa bata ganin bai kamata mata suyi limanci a addinin Musulunci ba, sai tace: Tace Al Qur'ani bai haramtawa mata yin limancin ba, sam sam. Bai ce mata ba za su iya jagorantar sallah ba.

Umarnin da Al Qurani ya bayar a bayyane yake kan cewa mata daya suke da maza a bangaren bauta.

"Sai dai su dinga hadawa maza shayi"

Da aka sake tambayarta shin baki ganin cewa hadisai ne suka haramta cudanya a tsakanin maza da mata, sai ta bada amsa kamar haka:

Tace a aikace abinda ke faruwa shi ne idan muka duba masallacin musulunci na farko, wanda manzon Allah Sallallahu Alihi Wa Sallam ya gina, zamu taras cewa wuri ne na al'umma inda maza da mata da yara kan je.

Kuma wuri ne da al'umma kan hadu. Amma bayan wadansu shekaru, sai masallatan namu suka kasance wuri da maza ne kadai kan hadu.

Inda ba a gayyatar mata da su je bangaren da maza suke. An mayar dasu can baya, sai dai su dinga hadawa maza shayi. Ba za su sami damar ganin limamin dake wa'azi ba.

Don haka yana da mahimmanci na sanarwa mabiya addini cewa Allah ne ya daidai ta matan don haka babu wani wanda zai kaskantar da su.

Wannan lamari dai na cigaba da daurewa jama'a kai, musamman musulmai, wadanda ke mamakin yadda jama'a ke sadaukar da imanin su domin cimma burin siyasa, ko kuma burge wasu al'umma.