An nuna shakku kan aniyar Isra'ila ta sassauta killacewar da ta yiwa Gaza

Image caption Isra'ila ta hana shiga da kayayyakin gini yankin Gaza

Kungiyoyin kasa da kasa sun nuna shakku dangane da matakin da Isra'ila ta dauka na sassauta killacewar da Isra'ailan ta yiwa Zirin Gaza.

Kungiyar Amnesty International ta ce tana marhabin da duk wani mataki na rage wahalhalun da mazauna yankin na Gaza ke sha, amma ta c e wajibi ne Isra'ila ta aiwatad da sokokin kasa da kasa ta hanyar dage datsewar da ta yiwa Gazan nan take.

Kungiyar ta Amnesty ta bayyana manufar ta Isra'ila da cewa tana hukunta duka al'ummar Palesdinawa ne.

Wakilin BBC ya ce shugaban Hukumar bada agaji ta majalisar dinkin duniya dake Gaza, John Ging ya ce abun da ya rage a gani yanzu, shi ne Isra'ila ta aiwatar da abun da ta fada a zahiri.

Sanarwar da Isra'ilar ta bada ta ce ta yi haka ne domin barin fararen hula da kayayyaki su samu shiga yankin Falasdinawa.

Wannan matakin da kasar ta dauka ya biyo bayan matsin lambar da take fuskanta game da killace Gazan da ta yi.

Kasashen duniya sun soki Sojojin Isra'ila game da harin da suka kaiwa jiragen ruwan da za su kai agaji Gaza a watan daya gabata.

Isra'ila da Masar sun killace Gaza ne bayan Kungiyar Hamas ta karbi mulki a yankin a shekarar dubu biyu da bakwai.

Majalisar zartarwar Isra'ila ta dauki wannan matakin sassauta killacewar ne bayan wata tattaunawa da tayi na tsawon kwanaki biyu.

Palesdinawa dai sun yi watsi da sanarwar da Isra'ila ta bayar, suna masu cewa farfaganda ce kawai.