Majalisun Amurka za su titsiye BP

Kamfanin mai na BP zai bayyana a majalisar dokokin Amurka
Image caption Shugaban kamfanin man BP,Tony Hayward

Majalisar dokokin kasar Amurka za ta yi tambayoyi ga shugaban kamfanin mai na BP,Mista Tony Hayward dangane da malalar mai a tekun Mexico.

Shugaban kamfanin na BP zai bayyana ne a majalisar dokokin,kwana daya bayan da kamfanin ya amince zai biya diyyar dalar Amurka biliyan ashirin ga mutanen da ke zaune a gabar tekun na Mexico, sakamakon lahanin da malalar man ta yi musu.

Shugaba Obama ya ce yanzu haka a karkashin dokokin Amurka akwai wani tanadi na dala biliyan saba'in da biyar da za a bukaci duk wani kamfanin hakar mai ya biya a duk lokacin da aka samu matsalar tattalin arziki sakamakon malalar man data haddasa gurbacewar muhalli makamancin wannan.

Malalar man dai ta jawo kace-nace tsakanin gwamnatin Amurka da kuma kamfanin mai na BP,abinda ake gani zai iya illa ga dangantakarsu.