Shugabannin Tarayyar Turai na taro kan tattalin arziki

Shugabannin Tarayyar Turai
Image caption Shugabannin Tarayyar Turai

Shugabannin kasashen kungiyar Tarayyar Turai suna tattaunawa a kan wasu tsauraran matakai na kaucewa sake aukuwar matsalar tattalin arziki a kasashen dake amfani da kudin bai daya na Euro.

Taron, wanda ake yi a birnin Brussels, yana duba yadda kasashen za su hada kai sosai wajen bullo da manufofinsu na tattalin arziki, wanda zai ba Tarayyar Turan damar sa ido a kan kasasfin kudin kasashen da kuma daukan tsauraran matakai kan kasashen da za su rika samun wagegen gibi a kasafin kudinsu.

Wakiliyar BBC ta ce shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta yi kiran da a fitar da wani matsayin bai daya domin gabatar da shi a taron kungiyar G20 da za a yi a makon gobe, wanda zai bada damar a saka wa duka bankuna haraji, ta yadda wadanda suka janyo wata matsalar tattalin arziki nan gaba, za su biya, fiye da kowa wajen shawo kanta.