Yarima ya bayyana a gaban hukumar NAPTIP

Nijeriya
Image caption Nijeriya

A Nijeria, yau ne dan majalisar dattawa Ahmed Sani, Yariman Bakura, ya bayyana a gaban hukumar NAPTIP mai yaki da fataucin mutane a kasar.

Hukumar dai ta ce ta kammala bincikenta dangane da zargin da aka rika yi cewa tsohon gwamnan na jihar Zamfara ya auri wata yarinya 'yar kasar Masar, wadda shekarunta ba su haura sha uku ba, yayinda shi kuma yake cewar shekarun nata sun haura haka.

To sai dai a bangare guda kuma, majalisar koli ta shari'ar musulunci ta shigar da kara a gaban kotu inda take neman fassarar kotun dangane da tanadin kundin tsarin mulki a game da huruminsa na auren karkashin dokokin shari'a.