An harbe wani makashi a Amurka

An zartar da hukuncin kisa a kasar Amurka
Image caption Shugaban Amurka,Barack Obama

An bindige wani BaAmirke har lahira a jihar Utah, bayan da aka same shi da laifin aikata kisan kai.

Wannan dai shi ne karo na uku da ake amfani da irin wannan hanya wajen zartas da hukuncin kisa a Amirka, tun bayan da kotun kolin kasar ta dawo da hukuncin kisa a shekarar 1976.

An dai bindige Ronnie Lee Gardner ne, bayan da aka yi watsi da karar karshe da ya daukaka.

Lauyan Mr Gardner ya ce ya zabi a bindige shi ne saboda ya nuna damuwa da irin matsalolin dake tattare da yin allurar guba.

Wasu dai sun soki al'ammarin, amma masu aiko da rahotanni sun ce babu wani kwakwaran yunkuri a Amirka na soke hukuncin kisan.

Kungiyoyin kare hakkin Dan Adam sun yi kakkausar suka a kan zartar da hukuncin kisan, inda suka bayyana shi da cewa jahilci ne.