An zartar da hukuncin kisa kan Ba Amurke

An zartar da hukuncin kisa a kasar Amurka
Image caption Shugaban Amurka,Barack Obama

An zartarwa wani Fursuna mai suna Ronnie Lee Gardener hukuncin kisa ta hanyar bindige shi a jihar Utah ta kasar Amurka.

Wannan shi ne karo na farko da aka zartar da irin wannan hukunci a kasar cikin shekaru goma sha hudu da suka gabata.

Zartar da hukuncin kisan dai ya biyo bayan zargin da aka yiwa Mista Gardener cewa ya kashe wani mutum shekaru ashirin da shida da suka gabata.

Kungiyoyin kare hakkin Dan Adam sun yi kakkausar suka a kan zartar da hukuncin kisan, inda suka bayyana shi da cewa jahilci ne.

Yunkurin Ronnie Lee Gardener a baya na neman a rage wannan hukunci zuwa hukuncin daurin rai da rai ya ci tura.