Za a cire 'ya'yan jama'iyu daga cikin hukumar zabe ta Najeriya

 Shugaba Goodluck Jonathan
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan

Shugaban kasar Goodluck Jonathan na Najeriya ya sha alwashin cire sunan duk wani dan jam'iya da aka gabatar da sunansa a matsayin kwamishina a hukumar zabe ta kasa.

Sai dai furucin shugaban ya zo ne a daidai lokacin da ake kace-nace a kan sunayen mutanen da ya gabatar wa majalisar dattawa domin nada su jami'ai a hukumar ta zabe.

Shugaban ya bayyana haka ne a wajen taron babban kwamitin zartaswa na Jama'iyar PDP na kasa karo na 51 da aka yi jiya a Abuja.

Shugaba Jonathan ya ce hakan zai kawar da matsalar zargi , duk da yake dai tsarin mulkin Najeriyar bai hana nada duk wani dan jama'iya rike mukami a hukumar zaben ba.