Shugabar riko ta Kyrgyzstan ta ziyarci birnin Osh

Shugaba Roza Otunbayeva
Image caption Shugaba Roza Otunbayeva ta Kyrgyzstan

Shugabar rikon kwariya a Kyrgyzstan, Roza Otunbayeva ta ce adadin wadanda suka rasa rayikansu a rikicin kabilancin da aka yi a kudancin kasar a makon jiya, zai kai kusan dubu biyu.

Adadin dai ya ninka har sau goma, kan wanda aka yi zato tun farko.

Ms Otunbayeva tana ziyara ne a yankin, a wani yunkuri na rage zaman zullumin da ake yi tsakanin 'yan kabilar Kyrgyz da na Uzbek marasa rinjaye.

Ta ce, suna so su tabbatarwa jama'a cewa za su sake gina wannan yanki, kuma mutane za su koma gidajensu,sannan su ci gaba da zama tare cikin lumana.

Dubun dubatar jamaa ne dai suka gudu daga gidajensu inda wasunsu suka tsallaka cikin Uzbekistan.

Shugaban Rasha, Dmitry Medvedev ya yi gargadin cewa rikicin na Kyrgyzstan zai iya as masu kishin Islama su karbe iko a kasar.