Libya za ta mayar da fursunon 'yan Nijar zuwa gida

 Gidan yarin Abu Salim na Libya
Image caption Gidan yarin Abu Salim na Libya

Gwamnatin kasar Libya ta amince ta mikawa Niger fursunoni 275 yan Nijar din da ke gidajen kaso a kasar Libya a wani bangare na yarjejjeniyar da kasashen biyu suka kulla.

A jiya ne dai jami'an gidan yarin Libyar suka bayyana haka yayin wata ziyarar Jami'an gwamnatin kasar ta Nijar.

Suka ce za a mika fursunoni 275 ga hukumomin Nijar wadanda 198 daga cikinsu an yanke masu hukuncin aikata manyan laifuka ne yayinda wasu sama da 70 ke jiran shara'a.

Hukumomin na Libya dai na rike da 'yan kasar ta Nijar 12 da ke jiran a aiwatar masu da hukuncin kisa.

Sai dai Jami'an na Libya ba su ce ga abinda zai faru gare su ba.

A kwanakin baya ne dai hukumomin na Libya suka aiwatar da hukuncin kisa a kan wasu yan Nijar din biyu.