Shugaban Sarkozy na ziyarar tarihi a London

Janar De Gaulle
Image caption Tsohon shugaban Faransa Janar De Gaulle, yana karanta jawabi a gidan rediyon BBC lokacin yakin duniya na biyu

Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy yana London domin halartar bikin cika shekaru saba'in da jawabin da Janar De Gaulle yayi ta gidan rediyon BBC lokacin yakin duniya na biyu.

A jawabin nasa Janar De Gaulle ya yi kira ga mutanen kasar sa da su tirje wa mamayen 'yan Nazi.

Mr Sarkozy din kuma ya haralci wani ofishin BBC da ake kira da Broadcasting House.

Shugaba Sarkozy ya fara yada zango ne a hedikwatar kafar yada labarai ta BBC dake tsakiyar London.

Inda shekaru saba'in da suka wuce janar Charles da Gwal yayi wata sanarwa ta sashin Faransanci ga mutanen Faransa, inda ya bukaci kada su bada kai ga mamayen 'yan Nazi.

Babban abinda ya faru a ziyarar aikin shugaban dai shi ne wani biki da akayi a Royal Hospital Chelsea.

Image caption Shugaba Sarkozy da matar sa, da kuma shugaban BBC Mark Thompson a gidan rediyon BBC

"Faransa na godiya ga Burtaniya"

Inda a kayi shawagi da jiragen saman da akayi amfani da su a yakin duniya na biyu.

Haka kuma agurin ne aka baiwa wasu 'yan mazan jiya 'yan Burtaniya da Faransawa shida lambar yabo.

Firai minista David Cameron yace kalaman Janar Gwal a shekarar 1940 kira ne daya janyo nuna jarunta.

Shugaba Sarkozy yace Faransa na godiya ga Birtaniya har abada da ta bar janar Gwal yayi sanarwar a nan London.