An kaddamar da asusun taimakawa Kyrgyzstan

Sakatare Janar na Majalisar dinkin duniya Ban Ki-Moon
Image caption Sakatare na majalisar dinkin duniya ya kaddamar da asusun dala miliyan saba'in da daya domin taimakawa wadanda rikici ya rutsa dasu

Sakatare janar na Majalisar dinkin duniya Ban ki-moon ya kaddamar da gidauniyar agajin gaggawa na dala miliyan saba'in domin tallafawa mutanen da rikicin kabilanci ya rutsa da su a Kyrgyzstan.

Majalisar dinkin duniya ta ce kimanin mutane miliyan guda ne ke bukatar taimakon abinci da ruwa bayanda kabilun Kyrgyz da Uzbek suka fafata da juna a kudancin kasar.

Hukumomin majalisar dinkin duniya sunce abin da za'a maida hankali wajen samarwa mutanen da rikicin ya shafa shine mahalli da kuma abinci kuma hukumomin suka ce suna fatan tallafin zai kai zuwa akalla watanni shida.

Gwamnatin Uzbeksitan ta nemi majaliasar dinkin duniya data kaddamar da wani asusun neman taimako irin wannan a sansanoninta a mako mai zuwa.

Ganin cewar ta amince da dubun dubatar 'yan gudun hijira shiga kasarta, fargabarta yanzu shine kada abinda take dashi na taimaka musu ya fara ja da baya