Obama ya yi murna da babban bankin China

Shugaba Obama
Image caption Shugaba Obama

Shugaba Obama yayi marhabin da sanarwar da babban bankin China ya bayar ta cewar sannu a hankali za ta kyale musayar kudadinta na Yuan ya kara zama marar tsauri.

Mr Obama ya kira sanarwar da cewar wani kwakkwaran mataki ne.

Sanarwar dai ta kasance babban labarin gidan TV na China:

Ta ce, mai magana da yawun babban bankin China a yau ya bayyana cewar yana da kyau a ci gaba da sauye sauye game da tsarin musayar kudin Yuan tare da kara sassauta darajar musayar kudin na Yuan.

'Yan siyasar Amurka dai sun jima suna bayyana cewar kudin na Yuan ba su da daraja, abinda ke baiwa China wata galabar cinikayyar da ba ta dace ba.

Sannan ana sa ran kuma manufar Chinar za ta fuskanci karin suka a taron shugabannin kasashe 20 da suka fi karfin tattalin arziki a duniya da za a yi cikin mako mai zuwa a Canada.