Alummar kasar Poland sun fara jefa kuri'arsu

An fara kada kuri'a a Poland
Image caption Wata rumfar zabe kenan da alummar kasar Poland suka taba kada kuri'arsu

Da sanyin safiyar nan al'ummar kasar Poland suka fara jefa kuri'a a zaben wanda zai maye gurbin marigayi shugaban kasa Lek Kachinski, wanda ya rasu a wani hadarin jirgin sama da ya hallaka jagororin siyasa da na sojin kasar a watan Afrilu a kasar Rasha.

'Yan takara goma ne suke neman kujerar shugabancin , ciki har da dan uwan tagwaitar Mr. Kachinski, Yaroswav.

Amma shugaban rikon kwarya Broniswav Komorowski shi ne kan gaba a adadin magoya baya.

Nan da mako biyu dai za'a yi zaben raba gardama idan aka rasa dan takarar da ya lashe rabin adadin kuri'un da aka kada.