Firaministan Turkiya zai yaki kungiyar PKK

Wani sojan kasar Turkiyya
Image caption Firaministan Turkiyya yasha alwashin yakar 'yan kungiyar PKK

Firiministan Turkiyya Rajab Tayyib Arduwan ya sha alwashin fatattaka kungiyar PKK ta Kurdawa 'yan aware.

Wannan na kunshe ne cikin sakon ta'aziyyar da ya aikewa shugaban sojin kasar bayan mutuwar sojoji goma sha daya a wasu harare guda biyu da PKK ta kai ranar Asabar daura da iyakar Turkiyya da Iraq.

Rundunar sojin Turkiyya ta baiyana cewa ta kai harin daukar fansa kan 'yan tawayen inda ta kashe akalla sha biyu daga cikinsu.