Mutane 26 sun mutu a Iraq

Fashewar bom a Iraq
Image caption Fashewar bom a Iraq

'Yansanda a Iraqi sunce an kashe mutane 26 sannan fiye da hamsin sun samu raunuka sakamakon wasu hare-haren bama-bamai a kananan motoci biyu a babbar kasuwar Bagadaza.

Bama baman sun tashi ne kusan tare , abinda ya haddasa mummnar barna ga wani banki mallakin gwamnati da kuma wani ginin ma'aikatar cikin gida inda mutane suke kan layin karbar fasfo da kuma katunan sheda.

Wani mazaunin birnin Mahmoud Assi ya bayyana cew bama-bamai dake a cikin kananan motoci biyu sun tashi daya bayan daya, sun kuma raunata galibin masu gadi ne.

Haka kuma wasu gidaje sun ruguje.

Wannan shi ne halin da ake ciki a babbar kasarmu Iraqi, Allah ya taimaka mana.

Harin ya zo ne mako guda bayan da aka kashe mutane 15 a Bagadaza a wani hari a babban bankin Iraqin.