Isra'ila za ta sassauta toshiyar Gaza

Gaza
Image caption Gaza

Isra'ila ta fitar da bayanin yadda za ta saukaka toshiyar da ta yiwa Zirin Gaza, tana mai cewar za a kyale dukkanin kayayyakin farar hula su shiga zirin.

Firaministan Isra'ila, Binyamin Netanyahu, ya ce Gwamnati za ta soke tsarin da ake da shi a halin yanzu na jeranta kayyakin da ake bari a shiga da su cikin Gazar, sannan ta maye shi da wani jerin kayan da aka haramta.

Ya ce za a bari a shigar da dukkanin kayan jin kai da na abinci, kamar kuma kayayyakin sarrafawar masana'antu da kuma kayan takamaimun ayyukan gini.

Isra'ila dai ta fuskanci tsananin matsin lamba daga kasashen duniya don saukaka toshiyar, bayan wani farmakin Isra'ila a kan jiragen ruwan dake dauke da kayan agaji zuwa Gaza makunni uku da suka wuce yayi sanadiyar mutuwar masu fafutika tara 'yan kasar Turkiyya.