Jama'ar Poland na kada kuri'ar zaben shugaban kasa

Zabe a kasar Poland
Image caption Zabe a kasar Poland

Jama'ar kasar Poland na zaben sabon Shugaban kasa, wanda zai maye gurbin Lech Kaczynski wanda ya mutu tare da shugabannin siyasa da na soji na kasar da dama, a lokacin da jirginsa ya fadi a Rasha cikin watan Afrilu.

Dan uwan tagwaicin Mr Kaczynski, tsohon Firaminista, Jaroslaw Kaczynski na Jam'iyar masu ra'ayin yan mazan jiya ta Law and Justice, na fatan gadonsa.

To amma wanda ke kan gaba shi ne Shugaba mai riko Brinislaw Komorowski, na jama'iyar masu ra'ayin jari hujja ta Civic Platform mai mulki.