An gano tarkacen jirgin daya bata a Congo

Jirgin sama
Image caption Daukacin fasinjan dake jirgin da aka gano a Congo sun mutu.

Ma'aikatan ceto a jamhuriyar Congo, sun gano tarkacen jirgin saman da ya bata tun ranar asabar din data gabata bayan tashinsa daga birnin Yaounde a jamhuriyyar Kamaru.

Ministan yada labaran Kamaru, Tchiroma Bakary, yace dukan wadanda ke jirgin goma sha daya ciki har da wani hamshakin mai kudi dan kasar Australia sun hallaka.

kodayake ba'a kai ga sanin abinda ya haddasa hadarin jirgin ba, ministan yace za'a sami karin haske game da hakan idan an gano bakin akwatin jirgin.

A ranar Asabar jirgin ya bata, bayan ya tashi daga birnin Yaounde, zuwa garin Yangadou a Congo-Brazzaville.