Juan Manuel Santos ya lashe zaben Colombia

Zababben shugabankasar Colombia Juan Manuel Santos
Image caption Juan Manuel Santos ya lashe zaben shugabankasar Colombia abinda zai bashi damar cigaba da manufofin Alvaro Uribe

Dan takarar jam'iyyar da ke mulkin Colombia, Juan Manuel Santos ya yi nasarar cin zaben shugabancin kasar.

A yayinda aka kidaya fiye da kaso casa'in da tara na kuri'un da aka kada, Mr. Santos ya yiwa abokin takararsa na jam'iyyar Green Party Antanas Mockus da sama da kaso arba'in.

Mr. Santos dai ya sha alwashin cigaba da ayyukan shugaba mai barin gado Alvaro Uribe tare da mai da hankali wurin murkushe yan tawayen kasar masu ra'ayin gurguzu da kuma yaki da safarar miyagun kwayoyi.

Mr Santos dai gogaggen dan siyasa ne wanda ya rike mukamin ministan kudi da kuma tsaro a kasar

Abokin takararsa dai ya taya alummar kasar Colombian murna