Kasashen E9 sun fara taro a Abuja

Taswirar Najeriya
Image caption Ministocin ilimi na kasashen E9 sun hallara a birnin tarayya Abuja.

Ministocin wasu kasashe tara da suka fi yawan jama'a a duniya, inda kuma jahilci yayi katutu wato E9, sun fara wani taron kwanaki hudu a Abuja, domin duba matakan shawo kan matsalar.

Kasashen dai sun hada da Nigeria, da India da China, da Pakistan, Bangladesh da dai sauransu.

Kashi sittin cikin dari na wadanda ke fama da jahilci a duniya na zaune ne a kasashen tara, kuma fiye da rabinsu mata ne.

A lokacin taron an mikawa Najeriya ragamar shugabancin kasashen tara na kungiyar ta E9.