Masana na sharhi kan kalaman Jonathan

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Image caption Batun tsayawa ko rashin tsayawar shugaba Goodluck Jonathan takara na cigaba da jan hankali.

A Najeriya, ana cigaba da tofa albarkacin baki dangane da rashin fitowar shugaban kasar, Dokta Goodluck Jonathan ya bayyana matsayinsa a kan ko zai tsaya takarar shugabancin kasar a zaben da za a gudanar a badi ko kuma ba zai tsaya ba.

Yayinda wasu masana harkar siyasa ke ganin kin bayyana matsayin nasa ya dace wasu kuwa ba sa goyon bayan hakan.

A wata hira da ya yi da manema labarai da aka watsa ta gidajen talabijin a ranar lahadi, shugaba Jonathan yace shi abinda ya sanya a gaba shine maida akalar kasar kan tafarkin da zai farfado da ita.

Tun bayan mutuwar marigayi shugaba Umaru Musa 'yaradua ne dai ake ta samun kungiyoyin dake fitowa suna neman Dr. Jonathan ya tsaya takara, yayinda wasu kungiyoyin ke sukar kin goyon bayansu ga tsayawa takarar shugabancin kasar a zaben 2011.