An kaddamar da asusun tallafawa Nijar

Asusun tallafawa masu fama da yunwa a Nijar
Image caption Kungiyoyin bada agaji biyu sun kaddamar da asusun gaggawa domin tallafawa masu fama da yunwa a jamhuriyar Nijar

Wasu manyan kungiyoyin bada agaji guda biyu sun kaddamar da gidauniyar agajin gaggawa domin tallafawa miliyoyin mutanen da ke fama da yunwa a jamhuriyar Nijar.

Kungiyoyin na Save the Children da Oxfam sun ce lokaci bai kure ba, a kokarin kaucewa sake faruwar yunwar da ta jefa kimanin mutane miliyan uku da rabi cikin halin kaka-ni-kayi shekaru biyar da su ka gabata a jamhuriyar ta Nijar.

Wakiliyar Majalisar dinkin duniya a jamhuriyar Nijar Khardiata Lo Ndiaye ta ce halin da ake ciki ya dara na farin shekara ta 2005.

Matsalolin da suka hada rashin kyawun amfanin gonar da aka samu a shekarar bara da kuma harhawar farashin kayayyaki ne suka jefa Nijar cikin halinda take ciki

Majalisar dinkin duniya ta nanata cewar ana bukatar kudaden da za'a tallafawa kasar ba tare da wani bata lokaci ba