Ciwon kumburin hanta a Kamaru

kwayar cutar hepatitis B
Image caption cutar kumburin hanta ta hepatitis na addabar jama'a da dama a Kamaru.

Gwamnatin Kamaru ta nemi hadin gwiwar kungiyoyi da dama, wajen fadakar da jama'a dangane da illar cutar kumburin hanta.

Wani bincike ya nuna cewa akwai mutane kimanin miliyan dubu biyu dake dauke da kwayar cutar hepatitis B, kuma mutane kimanin dubu dari biyar ne, ke mutuwa a sakamakon haka a duk shekara.

A nahiyar Afurka, kasashen Kamaru da Masar ne suka fi wadanda suka kamu da kwayar cutar.

A Kamarun hukumomi na cewa ana samun mutane goma a cikin dari, suna dauke da kwayar cutar.

Don haka suka tashi tsaye wajen fadakar da jama'a muhimmancin yin alllurar riga-kafi, da kuma da kuma sauran matakan hana kamuwa da cutar.