An mika sunan shugaban hukumar zabe ga majalisa

Shugaban Najeriya, Dr. Goodluck Jonathan
Image caption Shugaba Goodluck yayi alkawarin kawo gyara a harkar zaben Najeriya.

Fadar shugaban Najeriya ta mika sunayen shugaba da mambobin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ga majalisar dattawan kasar don tantancewa.

A farkon wannan watan ne majalisar kasa ta amince da sunan Farfesa Attahiru Jega a matsayin sabon shugaban INEC, tare da wasu mutanen da shugaban Najeriyar, Dr. Goodluck Jonathan ke so su zama kwamishinonin hukumar zaben.

Sai dai a cikin jerin sunayen da aka gabatarwa majalisar dattawan a yau babu sunayen mutane biyu daga ainihin sunayen da aka gabatar ga majalisar kasa.

Sake shugabancin hukumar zaben kasar dai na gaba-gaba cikin batutuwan da ke tattare da cece-kuce game da samun ingantaccen zabe a kasar.