'Yan Majlisar Najeriya za su tantance Jega

Farfajiyar Majalisar Dokoki ta Najeriya
Image caption 'Yan Majalisar Dattawan Najeriya za su karbi wasikar Shugaba Goodluck Jonathan mai dauke da sunayen kwamishinonin zabe

A Najeriya, yau ne 'yan Majalisar Dattawa za su koma bakin aiki bayan wani hutu da suka yi na makwanni biyu.

Daga cikin manyan abubuwan da ake sa ran za a gabatarwa Majalisar har da wata wasika daga Shugaban kasa Goodluck Jonathan mai kunshe da sunayen wadanda yake son nadawa a matsayin shugaba da kuma kwamishinonin hukumar zaben Najeriya.

Bayanai dai na nuna cewa wadansu daga cikin wadanda ake son nadawa a hukumar zaben suna da alaka da wadansu jam'iyyun siyasa, al'amarin da ya janyo suka, bisa la'akari da ikirarin shugaban kasar na tabbatar da cewa an yi zaben gaskiya da adalci badi.

Ba duk ‘yan Najeriya ne dai suka yarda da ikirarin na Shugaba Jonathan ba—har sai sun ga yadda ta kaya a Majalisar Dattawan.

Daya daga cikin ’yan siyasar kasar, Alhaji Alhassan Pau, ya shaidawa BBC cewa makomar fatan al’ummar Najeriya na samun zabe mai inganci na hannun ‘yan Majalisar.

“Abin da mu ke tsammani shi ne su ‘yan majalisa za su zartar da magan ta gari: da shi shugaban [hukumar zaben], da kwamishinonin da za a nada, to a sa mana na gari.

“Idan aka sa na gari, to mun yarda cewa zabe zai gyaru”, inji Alhaji Alhassan.

Daya daga cikin ’yan Majalisar Dattawan, Sanata Kabiru Ibrahim Gaya, ya bayyana cewa za su bi matakan tantance su a hankali, “saboda tun farko tunaninmu [da] burinmu shi ne mu canja tsarin zabaen Najeriya”.

Dan majalisar ya kuma ce: “Mu ba za mu bari wani dan jam’iyya ya zama kwamishinan zabe ba, saboda in ya tashi, jam’iyyar zai yi kokari ya kare mutuncinta, ba jama’a zai karewa mutunci ba”.

Haka nan kuma ana sa ran 'yan majalisar za su mayar da hankali a kan kudurin dokar nan a kan sake fasalta tafiyar da fannin hada-hadar man fetur a kasar.

Dokar dai ta zama tilas a cewar masu goyon bayanta, suna masu zargin cewa kudaden shigar da gwamnati ke samu daga man fetur bai kai yadda ya kamata ba.

To sai dai tun kafin a je ko ina an ruwaito kamfanin mai na Shell na cewa zai dakatar da ayukansa a kasar da suka kai dala dubu arba'in saboda dalilan da suka shafi aiwatar da wannan doka.

Wasu kamfanonin mai kuma na cewa watakila su fice daga kasar idan aka fara aiki da dokar.

Dokar dai ta tanadi yin sauyi ne ga tsarin ayyuka a bangaren man fetur, da kuma kara yawan kudin shigar da gwamnati ke samu daga man.