'Yan Majalisa sun ba hammata iska a Najeriya

Majalisar dokokin Najeriya
Image caption Majalisar dokokin Najeriya

A Najeriya, majalisar dokokin kasar ta koma zamanta inda aka bude zaman da hayaniya da dambe a majalisar wakilan kasar.

Wannan ya auku ne sakamakon sabani da aka samu tsakanin yan majalisar wadanda ke yunkurin tsige kakakin majalisar da kuma wadanda ke adawa da hakan.

Tuni dai aka dakatar da wadanda ke hankoron tsige kakakin majalisar wadanda ke kiran kansu The Progressives har zuwa karshen zaman majalisar na bana.

A lokacin da majalisar ta fara zaman ne dai Hon Chimeh Ingbawa ya tashi domin ya gabatar da wani kuduri wanda masu yunkurin tsige kakakin majalisar ke tsammanin cewa zai kasance ne kudurin dakatar da su, sai su ma shugabansu wato Hon Dimo Melaye ya tashi inda shi ma yayi kokarin gabatar da tasa kudurin.

Daga nan sai hayaniya ta kaure wanda har ya kai ga dambe tsakanin yan majalisar. Sakamakon wannan damben ne aka raunata Hon Doris Uboh da Hon. Solomon Ahwinahwi wanda ya samu karaya a hannu.

Daga nan kuma sai masu goyonbayan kakakin Majalisar Dimeji Bankole, suka fara korar yan majalisar dake yunkurin tsige kakakin majalisar su goma sha daya da karfin tsiya, inda har daga cikinsu har aka yayyaga masu kaya aka tunbuke masu huluna, wasunsu ma babu riga aka kore su daga majalisar.

Wakilin BBC wanda ya halarci zaman majalisar ya nemi ji daga wurin wadanda aka korar amma hakan bai samu ba saboda suna cikin wani yanayi ne tashin hankali.

Ya dai samu zantawa da daya daga cikin wadanda suka kori yan majalisar wato Hon Jeri Manwe ko me yasa suka dauki wannan mataki.

"Basu bi dokoki da majalisar ta shimfida ba, shiya ya sa muka dakatar da yunkurin da suke yi, Majalisa ta tanaji dokokin da za su mangance duk wani korafi game da majalisar". Inji Manwe.

Ana kan haka ne kuma sai yan sanda suka shigo inda manema labarai suka ke hango abin dake faruwa a cikin majalisar suka kama wasu yan jarida guda biyu bisa dalilin cewa bai kamata wai su rika daukar hoton abin dake faruwa ba.

Zaman majalisar dai ya ci gaba inda a halin yanzu aka tafi da wanda aka raunata zuwa babban asibitin kasa a Abuja.