Ma'aikatan kwasar shara sun shiga yajin aiki

Taswirar jamhuriyyar Nijar

A jamhuriyyar Nijar, ma'aikatan kamfanin HYSACAM mai aikin kwasar shara a birnin Yamai, sun shiga yajin aiki na sai abinda hali yayi.

Ma'aikatan na kokawa ne da ofishin magajin garin birnin da kewaye, wanda suka ce yana yunkurin durkusar da kamfanin na HYSACAM.

Hakan a cewar masu yajin aikin ya biyo bayan rashin zuba kudin a kamfanin HYSACAM da ya kamata ofishin magajin garin yayi a kowace shekara, inda shi kuma kamfanin ya kasa biyan ma'aikatan.

Sai dai hukumomin da'irar birnin Yamai sun ce a yanzu su ma ta kansu suke, domin ba su da kudaden da zasu ba kamfanin.